Miliyoyin mutane za su shiga-uku a 2016

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Igiyar ruwan za ta sa ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya, sannan ta ta'azzara farin da wasu bangarorin ke fama da shi.

Kungiyoyin agaji na duniya sun ce mai yiwuwa tasirin igiyar ruwa ta El Nino mai karfin gaske zai ci gaba da haifar da matsananciyar yunwa da cututtuka ga miliyoyin mutane a shekarar 2016.

Kungiyoyin sun ce igiyar ruwan za ta haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya, sannan ta ta'azzara farin da wasu bangarorin ke fama da shi.

A cewarsu, lamarin zai fi muni a nahiyar Afirka inda za a fuskanci matsanancin karancin abinci a watan Fabrairu.

Kazalika, yankuna irinsu Caribbean, da tsakiya da kuma kudancin Amurka za su fada cikin wannan mummunan hali nan da watanni shida masu zuwa.

Igiyar ruwan -- wadda ke aukuwa lokaci zuwa lokaci -- tana sa yanayi ya kara yin zafi, sannan ta rikita tsarin sauyawar yanayi, wanda hakan ne ma ya sa 2015 ta kasance shekarar da ta fi zafi tun da aka fara ajiye tahirin yanayi na duniya.