Australia: Wutar daji na ci gaba da ci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wutar daji a Australia

Wutar dajin nan da ta fara ci a lokacin bukukuwan kirsimeti,a Australia, har yanzu ta na ci gaba da ruruwa.

Yanzu haka, wutar dajin ta na ci ne a wajen garin Kennet River da ke kusa da Melbourne.

Kuma a na tsammanin wutar wacce ta lashe gidaje fiye da 100 a jihar Victoria, a ranar Kirsimeti, ta karu a wasu sa'o'i masu zuwa.

An bukaci al'ummomi garuruwa uku da ke kudancin Australia da su tashi daga gidajensu, bayan da aka kasa shawo kan wata wutar da take ci gaba da karuwa a yankunan.