Ina aka kwana kan wa'adin murkushe Boko Haram ?

Image caption Shugaba Buhari ya shaida wa BBC cewa sojoji sun yi galaba kan 'yan Boko Haram.

A ranar Alhamis ne wa'adin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin kasar domin murkushe kungiyar Boko Haram ke cika.

A watan Agusta ne dai shugaban ya ba su umarnin kawar da 'yan Boko Haram zuwa karshen watan Disambar da ke karewa a yau.

A hirar da shugaban ya yi da BBC a makon jiya, ya ce sojojin sun ci galaba a kan 'yan kungiyar, yana mai cewa yanzu Boko Haram ba ta kwace garuruwa da kauyuka kamar yadda ta saba yi a baya.

Shugaba Buhari ya kara da cewa kisan da sojoji ke yi wa 'yan Boko Haram ya sa ba a iya kai hare-hare sai dai su daurawa kananan yara mata bama-bamai, sannan su tura su cikin jama'a domin su tayar da su.

Sai dai duk da ikirarin da sojoji da mahukuntar Najeriya ke yi na yin gabala a kan 'yan Boko Haram, kungiyar na ci gaba da kai hare-hare, musamman na kunar-bakin-wake lamarin da kan yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Ko da a karshen makon jiya, 'yan kungiyar sun kashe mutane da dama a Borno da Adamawa.