Neville ba zai koma United ba nan kusa

Image caption Gary Neville ya ce zai kara jajircewa a matsayin sa na mai horas da 'yan wasan Spaniya.

Kociyan Valencia Gary Neville ya ce ba shi da burin jagorantar Manchester United ko kulob din Ingila a yanzu.

Neville ya ce zai ci gaba da jajircewa wajen bayar da horo ga 'yan wasan Spaniya, ba wai amfani da su a matsayin guzuma yana harbin karsana ba.

An dora Neville mai shekaru 40, a matsayin kociya a Mestalla ranar 2 ga watan Disamba, kuma yana mataimakin kociyan Ingila Roy Hodgson, kazalika ya buga wa United wasanni 602.

Ya shaidawa jaridar Daily Telegraph cewa, "Na tabbatar muku cewa ba zan zama kociyan Ingila ko Manchester ba nan da watanni shida"

Ya kara da cewa jita-jitar da ake yi ba ta da wata makama.