An shiga sabuwar shekara 2016 a Australia

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption An soke bukukuwan a wasu kasashen

Wasu kasashe a duniya sun soma bukukuwan shiga sabuwar shekara ta miladiyya, 2016 inda aka soma a kasashen Australia da kuma New Zealand.

Dubun dubatan mutane sun taru a dandalin Auckland Sky Tower inda aka yi wasa na tartsatsi da wuta.

Haka kuma an yi bukukuwa a Samao da Kiribati domin shigowar sabuwar shekara.

Sai dai an soke bukukuwan sabuwar shekara an kuma tsaurara matakan tsaro a biranen Turai da dama saboda fargabar tsaro

Tuni aka soke wasan tartsatsin wuta a Paris, amma za a kyale taruwar jama'a a dandalin Champs Elysees.

Ita ma gwamnatin Belgium ta soke bukukuwan a yayin da a Rasha, aka hana jama'a kaiwa dandalin Red Square.