An yanke wa Fasto hukuncin kisa a Rwanda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin Uwinkindi da hannu a kashe 'yan Tutsi

Babbar kotun Rwanda ta yanke hukuncin kisa, a kan wani limamin coci wanda aka zarga da aikata kisan kare-dangi da laifin cin zarafin bil-Adama shekaru 20 da suka wuce.

Kotun ta samu, Jean Uwinkindi ne da laifin jagorantar hare-haren da aka kai a kan 'yan kabilar Tutsi.

An tuhume shi da laifin ba da umarni a kashe mutane kusan 2,000 wadanda suka nemi mafaka a cocinsa.

Shi ne mutum na farko da aka zarga wanda kotun Majalisar Dinkin Duniya mai mazauni a Tanzania wacce ke hukunta laifukan da suka shafi kisan kare dangi ta mayar Rwanda don a yi masa shari'a.