Basarake a Afrika ta Kudu zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An shafe dogon lokaci ana shari'a kafin a yanke wa Sarki Dalindyebo hukunci

Wani Basarake a Afirka ta Kudu, zai fara zaman kaso na shekaru 12 bayan da aka same shi da laifukan tayar da gobara da kuma cin zarafin mutane shekaru goman da suka wuce.

Sarki Buyelekhaya Dalindyebo ya gaza samun nasara a karar da ya shigar, wadda ta dauki dogon lokaci a kan hana a daure shi.

An same shi ne da laifin cinna wuta a wata gona saboda yana san tashin mutanan da ke zama a wajen.

Sarkin dai ya ce ya yi kokarin ladabtar da al'ummarsa ne.

Wani alkali ya yanke hukuncin cewa sarkin bai fi karfin doka ba, kuma tilasne ya yi zaman kaso.