Twitter ya sabunta dokokin hana cin zarafi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Shafin Twitter

Kamfanin shafin Twitter ya sabunta dokokinsa, a wani mataki na nuna cewa ya kuduri daukan tsauttsauran mataki game da masu batanci a shafin.

Hakan ya biyo bayan zargin da ake yi wa shafin na Twitter ne akan cewa ya ki daukan matakan hana cin mutunci ko batanci da kuma yada kalamai na tsattsaurar akida.

A bayanin daya wallafa, kamfanin na Twitter ya ce bisa sabbin dokokin, ba za a sake lamuntan wani yayi amfani da shafin don cin zarafin wasu ba.

Haka zalika, kanfanin ya ce ya ware nau'o'in kalamai da za a tuhumi wadanda suka yi su a matsayin suna yunkurin cin mutuncin wasu.

Sun kuma hada da

- Yin barazanar fitina ga wasu, ko yada wasu kalaman cin zarafi daga wani shafi da aka dakatar. - Amfani da sunayen wasu mutane da nufin yin damfara ko cuta.

Kamfanin na Twitter ya sha alwashin rufe shafukan mutanen da suka sabawa sabbin dokokin da ya gindaya.