An kori Musulmi 200 daga aiki saboda Sallah

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Somalia, Omar Jamal, ya ce dole ne kamfanoni su fahimci cewa Musulunci ya bukaci mabiyansa su rika yin sallah sau biyar a kowacce rana.

Wata masana'antar sarrafa nama a birnin Colorado na Amurka ta kori ma'aikatanta Musulmi 200 bayan sun yi bore saboda an kirkiro wata doka da suka ce za ta hana su yin sallah a lokutan aiki.

Akasarin ma'aikatan 'yan kasar Somaliya ne da suka je Amurka domin yin aiki.

Kakakin kungiyar Musulmin Amurka Jaylani Hussein ya ce a wasu lokuta ne kawai ake kyale ma'aikatan su rika yin sallah.

Sai dai kakakin masana'antar ta Cargill Meat Solutions ya ce an gina gidan da ma'aikatan za su rika yin sallah, ko da ya ke ya kara da cewa dole ma'aikatan su bi sharudan da masana'antar ta gindaya kafin su yi amfani da wurin.

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Somaliya, Omar Jamal, ya ce dole ne kamfanoni su gane cewa Musulinci ya bukaci mabiyansa su rika yin sallah sau biyar a kowacce rana.