An kai hari sansanin sojin sama a India

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan sanda a India

'Yan sanda a India sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani sansanin sojin sama da ke kusa da iyakar kasar da Pakistan.

Jami'ai sun ce maharan sun yi amfani da wata karamar motar 'yan sanda da suka kwace wajen kaddamar da harin a sansanin sojin saman da ke Pa-than-kot.

Rahotannin farko-farko da aka samu sun nuna cewa an kashe wasu daga cikin 'yan bindigan, yayin da aka yi wa sauran zobe.

Rahotannin sun kuma ce ana ci gaba da jin karar harbe-harben bindiga daga cikin sansanin sojin.

An tura sojojin kundunbala da jiraje masu saukar angulu wurin da lamarin ya auku.

Harin dai ya zo ne 'yan kwanaki da ganawar Firayiministan India, Narendra Modi da takwaransa na Pakistan, Nawaz Sharif a Lahore, domin kaddamar da wani shirin bazata na zaman lafiya.