IS: An kai wa sojin Iraki hari a Ramadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojin Iraki na kokarin kwato iko da birinin Ramadi, daga kungiyar IS.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba na cewa wasu mayakan kungiyar IS sun kai hari a kan wani sansanin soji da ke arewa da birnin Ramadi, inda aka kashe sojojin gwamnati sittin.

Wani jami'in rundunar sojin kasa ta Iraki ya ce wasu 'yan kunar-bakin-wake da suka yi damara da bama-bamai a motoci ne suka jagoranci kai harin, lamarin da ya tilastawa sojojin janyewa.

Ya kuma ce daga bisani sojojin sun mayar da martani ta taimakon jiragen saman yaki na kawancen kasaskehn da ke yakar kungiyar ta IS.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Iraki ke yunkurin fadada ikonsu a birnin na Ramadi.