Isra'ila: An kai hari a Tel Aviv

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun ce basu san dalilin kai wannan hari da dan bindigan ya kai wata mashaya a birin Tel Aviv da ke kasar Isra'ila ba.

Akalla mutane biyu ne suka mutu aka kuma raunata wasu bakwai, a wani hari da aka kai birnin Tel Aviv da ke kasar Isra'ila.

'Yan sanda sun bayyana cewa wani dan bindiga ne ya bude wuta a kan wani taron jama'a a wata mashaya da ke tsakiyar birnin.

Jami'an tsaron dai sun ce har yanzu ba su san dalilin wannan hari ba, sun kuma ce an tsaurara tsaro a birnin gabanin bikin shigowar Sabuwar Shekara, ba su ga wata alamar da ke nuna cewa za a kai hari ba.

Jami'an tsaron sun kaddamar da wani gagarumin aikin binciko dan bindigar da ya tsere bayan da ya aikata wannan hari, inda aka toshe hanyoyin shiga da fita daga gine-gine a yunkurin kamo shi.