Kagame ya amince ya yi ta-zarce

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Kagame ya danne kowa a siyasar Rwanda tun bayan da sojojinsa suka kawo karshen kisan kare dangi a kasar a 1994.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya tabbatar da cewa zai sake neman shugabancin kasar a karo na uku a shekara ta 2017.

A jawabinsa na sabuwar shekara, Mista Kagame ya ce 'yan kasar sun nuna suna so ya ci gaba da jagorancin kasar, yana mai cewa ba zai watsa musu kasa a fuska ba.

Sai dai ya ce Rwanda ba ta bukatar a ce mutun daya ne tal zai jagorance ta har abada, sannan ya kara da cewa dole nan gaba wani ya karbi mulki daga hannunsa.

A kwanakin baya ne 'yan kasar suka kada kuri'ar raba-gardama inda suka amince da gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bai wa Mista Kagame damar iya ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2034.

Shugaba Kagame ya danne kowa a siyasar Rwanda tun bayan da sojojinsa suka kawo karshen kisan kare dangi a kasar a 1994.