Rouhani ya soki kona Ofishin Jakadancin Saudiya

Hassan Nasrallah
Image caption Shugaban Kungiyar Hezbollah ta Lebanon

Shugaban Kungiyar Yan Shi'a ta Lebanon, Hezbollah, ya yi kakkusar suka a kan Yan Saudi game da kisan Nimr al-Nimr.

A cikin wani jawabi ta Talabijin Hassan Nasrallah ya ce yan Saudiya na son haddasa hushuma tsakanin yan sunni da kuma yan shi'a a ko'ina cikin duniya, sannan ya bukaci yan shi'a da kada su mayar da martani ta yadda ya ce zai yi daidai da manufar makasan Shehin.

Tun farko dai Shugaba Hassan Rouhani na Iran yayi tir da wadanda suka kai hari a kan ofisoshin jakadancin Saudiya a Tehran da duk wasu wurare a cikin kasar.

Tashin hankalin dai wani martani ne game da kashe wani Malamin Shi'a, Sheikh Nimr al-Nimr ne da Saudiya ta yi.

Shugaba Rouhani ya ce abunda Saudiyar ta yi zai tayar da zaman dar dar din addini, to amma Iran ba za ta bar yan kasarta su aikata ababuwan da ba su kan ka'ida ba.

An kama mutane 40 da ake zargi da hannu a hare hare a kan wuraren diplomasiyar.