Somalia:Harin kunar bakin wake a Mogadishu

Wani dan kunar bakin wake sanye da kwat da ya yi shiga kamar dan kasuwa ya tarwatsa kansa a wani gidan cin abinci a Mogadishu babban birnin Somalia inda ya hallaka kansa da kuma wani mutum guda.

Wadanda suka shaidar da lamarin sun ce wasu yan jarida da ke shan shayi a gidan cin abincin sun gudu bayan da suka lura da mutumin wanda basu amince da shi ba da wata waya rataye a kirjin sa.

Wannan shine karo da ake kai hari a gidan cin abincin wanda baki yan kasashen waje kan ziyararta a kai a kai.

Kungiyar al Shabab ta kai harin bama bamai da dama a Mogadishu duk da fatattakar su da aka yi daga birnin a shekarar 2011.