Yemen:Yarjejeniyar tsagaita wuta ta ci tura

Kawancen da Saudiyya ke jagoranta da ke fafatawa da mayakan Houthi a Yemen ya sanar da cewa ba zai sake amincewa da tsagaita wuta ba.

A cikin wata sanarwa kawancen yace yan tawayen sun kai hare hare da dama a kan iyakokin saudiyya sun kuma harba rokoki a cikin biranen Saudiyya.

Ana samun yawaitar hare hare a kusan kowace rana, lamarin da ya saba yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da nufin bada damar tattaunawar tsagaita wutar na dogon lokaci.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi amannar cewa mutane kusan dubu shida ne aka kashe tun bayan da kawancen hadin gwiwar ya kaddamar da farmaki a watan Maris din bara.

Yan tawayen Houthi wadanda ke samun goyon bayan Iran su ne ke iko da kusan rabin kasar Yemen.