Selfie ya fallasa dan fashi a California

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption `yan sandan California

'Yan sanda a jihar California ta Amurka sun ce sun cafke wani da ake zargin dan fashi da makami ne da taimakon irin hoton nan na zamani da mutum kan dauki kansa, wato selfie, wanda mutumin ya dauka da daya daga cikin mutanen da ya yi wa sata.

'Yan sandan sun ce mutumin dan shekara 18 da haihuwa mai suna Almanza-Martinez yana daga cikin wasu mutum uku da suke zargi da yi wa wasu mutum hudu satar mota da kaya a mankon jiya.

Sun ce sun gano cewa wanda ake zargin sai da ya yi magana da wata mata daga cikin wadanda aka yi wa satar, ya kuma dauki hoton selfie da ita kafin ya tsere da abin da ya sata.

A cewar 'yan sanda, da taimakon hoton ne suka bi shi, kana suka cafke shi, kuma a halin da ake ciki suna tuhumarsa da fashi da makami da kuma satar mutane.