Kasashen Larabawa sun dauki mataki kan Iran

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Bahrain saboda kashe malamin Shi'a

Dagulewar huldar diflomasiyya a gabas ta tsakiya ta kai matuka bayan da Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa a kan wani Malami dan Shi'a.

Kasashen Larabawa na ci gaba da yanke huldar jakadanci tsakaninsu da Iran.

Bahrain da Sudan duk sun yanke huddar jakadanci da Iran a yayin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta rage karfin huldar ta da Iran din.

Wadannan kasashen uku sun dauki wannan matakin ne domin marawa kasar Saudiyya baya, wacce ta bai wa ma'aikatan jakadancin Iran kwanaki biyu su fice daga cikin kasar.

Iran na zargin Saudiyya ta kokarin janyo zaman dar-dar a yankin.

'Saudiyya ta kori jami'an Iran'

Gwamnatin Saudiyya ta bai wa ma'aikatan jakadancin Iran da ke kasar kwanaki biyu su fice daga kasar bayan ta yanke huldar jakadanci da ita sakamakon sabanin da kasashe biyun suka samu bayan zartar da hukuncin kisa a kan wani fitaccen Malamin Shi'a, Sheikh Nimr al-Nimr.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ofishin Jakadncin Saudiyya da aka kona a Tehran

Ministan harkokin wajen Saudiyya Adil Al Jubair ya zargi Iran da kafa wasu gungun 'yan ta'adda tare da raba musu makamai a yankin.

A ranar Asabar din da ta gabata ne masu zanga-zanga suka far ma ofishin jakadancin Saudiyya da ke Tehran, domin nuna fushinsu game da kisan da aka yi wa Sheikh Nimr al-Nimr da wasu mutum 46, wadanda aka ce an kama su da laifin ta'addanci.

Mahukunta a Iran dai na kallon Malamin a matsayin wanda ya yi shahada, wanda kuma ya goyi bayan zanga-zangar lumana.