Amurka ta rufe sansaninta a Habasha

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption us war plane

Amurka ta ce ta rufe sansanin jiragen yakinta marasa matuka da ke kasar Habasha.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Addis Ababa, babban birnin kasar ya ce a halin da ake ciki ba a bukatar jiragen yaki da sauran kayan fadanta da ke Arba Minch, mai tazarar kusan kilomita 400 daga Addis Ababa.

A shekara ta 2011 ne Amurka ta fara amfani da sansanin wajen kai hari kan mayakan Al Shabab da ke Somaliya.

Kasar Habasha dai kawa ce ga Amurka a gabashin Afirka, kuma ta tura daruruwan rundunonin sojinta kasar Somaliya domin su yaki Al Shabab.