Shin yin kalaci bata lokaci ne?

Hakkin mallakar hoto Getty

Kalaci ne abinci mafi muhimmanci da ake ci a rana - yana taimakawa wajen kara kuzari da kuma rage kiba.

Ko da ya ke haka aka shaida mana.

Amma masana kimiyya sun musunta wannan jita -jitar.

Shin ya kamata mu dauki kalaci da muhimmanci?

Bincike da dama sun nuna cewar masu kiba sun fi tsallake kalaci.

Amma kuma hakan zai iya zama illa.

Wannan dangantakar za ta iya samun nasaba da wani abu musamman kan karin kumallo - ko kuma mutanen da suke yi sun fi kuzari kuma sun fi bin ka'idojin cin abinci kuma suna kokari su ga sun yi rayuwarsu cikin koshin lafiya.

Duk da cewar a muna amfanin karin kumallo a ingantaciyyar rayuwa, wani rahoto da hukumar sa ido a kan masu kiba sosai ta Biritaniya, National Obesity Observatory, ya yanke shawarar cewar, ba za a iya bayyanawa ba ko akwai wata dangataka tsakanin nauyin jikin mutum ko kuma kalaci na daga cikin wasu rukunan abubuwan rayuwa da ke taimakawa wajen sa nauyin jiki.

Gwaji a kan kalaci

Gwaje-gwaje kadan da aka yi wadanda suka sauya yanayin cin abincin mutane ba su yi wani tasiri ba a kan fadin kugunsu.

Wani rahoto da aka wallafa a mujallar Amurka kan nau'kan abinci wanda aka yi wa lakabi da "mafi girma" ya bayar da shawara ga mutane masu kiba sosai guda 300 su daina ko kuma su rika yin kalaci na tsawon watanni hudu.

Farfesa David Allison, wanda ya gudanar da gwajin a Jami'ar Alabama, ya ce ba a samu bambanci ba ko kadan a raguwar nauyin jikinsu.

Ya ce mai yiyuwa wadanda suke tsallake karin-kumallo suna so ne su rage nauyin jikinsu ne kawai

Kuma wani hadari da ke tare da masu tsallake karin kumallo wanda kuma suke komawa yin kallacin zai iya sakawa su kara kiba idan har ba su rage yawan abincin da su ke ci ba da rana.

Hakan na nufin shawarar gwamnati ba daidai ba ce?

A ra'ayin Farfesa Allison: "Idan suna ba da shawarar kin cin kallaci a matsayin taimakawa wajen rage kiba, to wannan ba shi wani fa'ida".

Dr Alison Tedstone na daga cikin 'yan kungiyoyin duniya da suke cewa karin kumallo na da muhimmanci kuma tana nuni da gwajin da ya yi nuni cewar mutanen da suke tsallake kalaci sun fi kiba, wanda mun riga mun san cewar hakan na da dangantaka da ita.

Wanne karin kumallo ne mafi inganci?

Hakkin mallakar hoto

Babu wani abu musamman da ke nuna cewa ga kalacen da ya fi inganci, amma Dr Tedstone ya bayar da shawarar mutane su yi kalace da kayan abinci da zai yi saurin narkewa.

Ta ce mutane ba su cin isasshen kayan abinci da suke saurin narkewa a ciki kuma shi ne ma fi sauki a karin kumallo.

Farfesa Susan Jebb, wanin masanin kimiyya a jam'iar Oxford ya ce, hakan yana da matukar wahala.

Ta ce ya kamata a duba takardar da ake likawa jikin kayan abinci saboda wasu su na da karin sukari, ta ce kayanb lambu busassu ko kuma wadanda aka saka a miya suna karawa abinci dandano.

Zan bai wa mutane shawar su rika shan 'ya'yan itatuwa a lokacin karin kumallo - saboda gwara mutun ya ci kayan lambu a maimakon ruwan cikin 'ya'yan itatuwa saboda suna taimakawa wajen narkar da abinci.