Al-Shabab: An sake bude jami'ar Garissa

Image caption Sai an binciki mutum kafin ya shiga jami'ar

An sake bude Jami'ar Garissa ta kasar Kenya, watanni tara bayan da mayakan kungiyar al-Shabab suka hallaka mutane kusan 150 a jami'ar.

Ma'aikata sun koma aiki, a yayin da ake sa ran dalibai za su koma karatu a ranar Litinin mai zuwa.

An girke 'yan sanda a jami'ar domin tabbatar da tsaro.

Harin na al-Shabab a jami'ar, shi ne mafi muni da kungiyar masu jihadi ta kai a cikin kasar Kenya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dalibai na murnar koma wa makaranta

Kungiyar ta ce ta kai harin ne a wancan lokacin, a matsayin ramuwar gayya a kan gwamnatin Kenya wacce ta shiga kasar Somalia a shekara ta 2011 domin yakar kungiyar.