Niger: An bankado daruruwan rumfunan zabe na bogi

Image caption Tutar kasar Niger

A jamhuriyar Nijar, kwararru daga kungiyar kasashen da ke mu'amala da harshen Faransanci sun mika sakamakon binciken kundin masu zaben da suka yi, wanda ya bankado daruruwan rumfunan zabe da ba su da masu zabe, da kuma yaran da aka musu rajistar zabe alhali shekarunsu ba su kai ba.

A ranar Litinin ne dai aka mika sakamakon, kuma Hukumar zaben kasar mai zaman kanta, wato CENI ce ta bukaci a gudanar da binciken, don inganta harkar zabe, tare da samun karbuwa a tsakanin bangarori da lamarin ya shafa.

Binciken ya gano cewa an shigar da rumfunan zabe na bogi 323, yayin da aka yi wa kananan yara sama da 39,000 rajistar zabe, alhali ba su cancanci kada kuri'a ba.

An kuma yi wa mutane sama da 25,000 rajista fiye da sau daya.

Jam'iyyun siyasar Nijar ne dai suka bukaci a gudanar da wannan binciken a kan kundi ko rajistar masu zabe, kuma wasu daga cikin jam'iyyun sun shaida wa BBC cewa sun ji dadi da aka gudanar da shi, kuma suna fata mahukuntan kasar za su gaggauta yin gyara.

A watan Farairun gobe ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Nijar.