Zidane ya zama kocin Real Madrid

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Sabon Kocin Real Madrin, Zidane

Kulab din kwallon kafa na Real Madrid ya ce ya nada tsohon Keftin dinsa , wato Zinedine Zidane a matsayin sabon Kocin kulab din.

Zinadine Zidane dai ya maye gurbin Rafa Benitez ne, wanda aka sallama bayan wata bakwai da kama aiki, kuma Zidanen ya sha alwashin cewa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin kulab din ya ci kofi a karshen kakar wasanni.

A yanzu dai Real Madrid ne na uku a gasar La Liga, inda yake rufa-baya ga Atletico Madrid da Barcelona.

Tun wani kayen ci hudu da nema a watan Nuwamba da kulab din Barcelona ya yi wa Madrid, Rafa Benitez ke fuskantar matsin-lamba.

Real Madrid dai ya sha zama Zakaran Turai har sau goma, kuma Mujallar Forbes ta ayyana shi a matsayin kulab din kwallaon kafa mafi daraja a duniya.