Shinkafa da kwakwa hadari ne ga malmo

Image caption rice farms

A yankin kudu-maso-gabashin Asiya bunkasa noman shinkafa da kwakwar manja na barazana ga itatuwan daji irin su malmo da dangoginsa, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2012 gonakin shinkafa da na itacen kwakwar manja sun mamaye kashi 38 bisa 100 na jejin da ke dauke da itacen malmo da makamantansa, abin da ya haifar da rashin itace kamar yadda binciken ya sanar.

Yanki mai itacen malmo na da muhimmamci ga al'ummar da ke rayuwa bakin gabar teku saboda a nan ne al'ummar ke samun makamashi da kuma abinci.

Binciken na hukumar kimiya ya nuna cewa kiwon abubuwan ruwa ya kara haddasa rashin itatuwa masu nasaba da malmo a yankin musamman a kasashe kamar su Thailand da Philippines, kamar yadda daya daga cikin wadanda suka gudanar da binciken Daniel Richards na jami'ar kasar Singapore ya bayyana.