Saudiyya: Rikicinmu ba zai shafi Syria ba

Image caption Ministan harkokin wajen Saudiyya

Kasar Saudiyya ta musanta cewa sabanin da ke tsakanin da Iran zai shafi kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a yankinsu.

Jakadan Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya, Abdallah Al-Mu'allimi ya ce kasarsa za ta kara himma wajen dawwama zaman lafiya a kasar Yemen da Syria:

Ya ce a namu bangaren ba zai shafe mu ba, saboda za mu ci gaba da sa-himma wajen goyon bayan duk wani kokari na wanzar da zaman lafiya a Syria da Yemen da duk inda ake bukatar hakan.

Jakadan Ya ce za a iya magance rikicin idan Iran ta daina yin shisshigi ga al'amuran da suka shafi wasu kasashe.

Kasar Saudiyya dai ta yanke huldar Jakadanci da Iran, bayan masu zanga-zanga sun far ma ofishin jakadancinta da ke Tehran, a ranar Asabar din da ta gabata.

Masu zanga-zangar dai sun fusata ne bayan hukuncin kisan da Saudiyyar ta zartar a kan wani fitaccen malamin Shi'a.