Za a soma koyar da harshen Chinese a Tanzania

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Harshen Chinese na kara farin jini a duniya

Tanzania za ta soma koyar da harshen Chinese a wasu makarantun kasar, a wani mataki na kara kulla dangantaka da kasar China.

Gwamnatin Tanzania ta zabi wasu makarantun sakandare in Dar es Salaam da Dodoma da kuma birnin Morogoro da ke gabashin kasar domin soma koyar da shirin.

Kasar Tanzania din ta ce har ta dauki malamai 12 aiki domin su koyar da harshen na China.

China na daukar dawainiyar ayyukan gine-gine a kasar Tanzania.

Kasashen China da Tanzania sun dade suna da hudda a tsakaninsu tun lokacin turawan Biritaniya na mulkin mallaka.