Gobara ta yi barna a babbar kasuwar Yola

Image caption Kasuwanni da dama sun kone a Nigeria

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Yola da ke jihar Adamawa, lamarin da ya janyo hasarar dukiya mai dinbin yawa.

Bayanai sun ce matsalar wutan lantarki ce ta haddasa gobarar wacce ta shafe sa'o'i tana ci.

Rahotanni sun ce gobarar ta lakume kusan daukin kasuwar ta Yola, a yayin da galibin shaguna suka kone kurmusa.

Lamarin zai iya shafar yadda ake samun kayayyakin abinci a Yola, gannin cewa a kasuwar ake sayar hatsi kamar shinkafa da masara da wake da saraunsu.

Gobarar a kasuwar Yola na zuwa ne kwana guda bayan da wata gobarar ta tashi a kasuwar Abdulkadir Kure da ke Minna a jihar Niger.