Mutane 34 sun nutse a tekun Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An ceto wasu 'yan ci rani da dama

Akalla mutane talatin da hudu ne su ka nutse a tekun kasar Turkiyya, bayan da kwale-kwalen da suke ciki, ya samu matsala a hanyarsu ta ketarawa zuwa kasar Girka daga tsuburin Lesbos.

Babu takamaiman yawan kwale-kwalen da suka suka nutse a tekun na Aegean, sai dai hukumomin kasar Turkiyya sun ce an gano gawawwakin mutanen a kan yashin da ke gabar tekun, ya yin da wasu kuma ke yawo a saman ruwa.

Joel Millman shi ne mai magana da yawun hukumar da ke sa ido kan masu kaura ta duniya, ya shaidawa BBC cewa har yanzu 'yan ci rani na ci gaba da tururuwa dan ketarawa kasar Girka duk da tsakanin sanyin da ake yi.

Ya ce "Kusan baki 'yan ci rani da 'yan gudun hijira 2500 ne ke shiga kasar girka a kowacce rana daga kasar Turkiyya, wanda hakan ya kusan kai wa adadin da suke shiga a rana a watan Disambar bara."