Halliru ya bayyana gaban kotu a keken guragu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Halliru a lokacin kamfe tare da tsohon shugaba, Goodluck Jonathan

An gurfanar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bello Halliru da dansa Abba Muhammad a gaban babbar kotu a Abuja, bisa zarginsu da yin sama da fadi na kimanin naira miliyan 300.

Ana zargin sun karbi kudin ne daga ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara Sambo Dasuki, cikin kudaden da Dasukin ya shaida wa kotu cewa an ware su ne domin sayen kayan yaki.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ce take gurfanar da su a gaban kotun tare da kamfaninsu mai suna Bam Properties.

Rahotanni sun ce Bello Halliru ya isa kotun ne a kan keken guragu, a dalilin bashi da cikakkiyar lafiya.

Hakkin mallakar hoto EFCC

Bayanai sun ce shi ma kakakin jam'iyyar PDP, Olisa Metuh ya amsa tambayoyi gaban EFCC, bisa zarginsa da hannu a wata badakalar kudi.