Mata 'yan Shi'a sun yi muzahara a Kaduna

Image caption Matan sun ce suna son a mikawa musu gawawwakin 'yan uwansu

Mata mabiya akidar Shi'a a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, sun gudanar da zanga-zanga saboda rashin ba su gawawwakin 'yan uwansu da aka hallaka a rikicinsu da sojoji a Zariya.

Masu zanga-zangar dai na cewa kimanin makonni uku da faruwar rikicin, har yanzu ba su karbi gawawwakin iyalansu ba.

A wani taron manema labarai a Kaduna, 'yan kungiyar Islamic Movement din sun nuna damuwa a kan cewar har yanzu hukumomi ba su saki jagoran kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ba.

Gwamnatin Najeriya ba ta bayyana adadin mutanen da suka rasu ba a rikicin, amma dai mabiya mazhabar Shi'a din na cewa daruruwan 'yan kungiyar su aka halaka.

Wasu rahotanni sun ce an mika El-Zakzaky a hannun 'yan sanda domin gabatar da shi gaban kuliya.

Tuni gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike a kan rikicin.