An yanke wa Abdul Inyass hukuncin kisa

Wata babbar kotun shari'a a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta yanke wa Abdulaziz Dauda wanda aka fi sani Abdul Inyass hukuncin kisa.

Kotun ta same shi da laifin kalaman batanci ga Annabi Muhammadu SAW, da kuma tayar da hankali.

A karshen watan Mayun bara ne, a wajen wani maulidin Shehu Ibrahim Inyass a Kano, Malam Abdul Inyass ya yi kalaman da suka tayar da hankula har kuma aka tuhume shi da wasu mutane tara da laifukan da suka saba wa dokokin jihar ta Kano.

Tun a bara dai kotun ta yanke wa sauran mutanen tara, hukuncin kisa bisa samun su da laifukan amma sai aka jinkirta hukuncin ga Abdul Inyass wanda shi ne babban wanda ake tuhuma da laifukan.

An dai gudanar da shari'ar ce a cikin sirri.

Mutanen dai suna da damar daukaka kara a kotun gaba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga rahoton wakilinmu, Yusuf Ibrahim Yakasai daga Kano