An samu dabarar ceton Guza daga Burduddugi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Burduddigi

Masana Kimiyyi a Australia sun gano wata hanyar taimaka wa Guza yanda zai tsira daga sharrin Burduddigi mai guba, wanda danginsa ke jikkata wasu dabbobin dajin kasar.

A halin da ake ciki dai yawan Guzojin da ke kasar na raguwa saboda yaduwar Burduddigi mai guba, wadanda Guza kan bakunci lahira idan ya hadiye su, saboda dafin da ke jikinsu.

Yanzu masana kimiyya sun fita wata dabara ta hanyar koya wa Guza yanda zai daina yin kalaci da Burduddigi, inda aka samar da wasu kanana, wadanda ba su da dafi sosai, aka kuma koya wa Guzojin hadiyar su.

Ko da Guzojin sun hadiyi kananan Bududdigan ba sa mutuwa, sai galabaita kawai, inda daga bisani sukan koma hayyacinsu.

Kuma daga nan sukan kiyaye ko da sun ga Burduddugi a gaba ba sa hadiyar sa, saboda sun san hadarin da ke tattare da yin hakan.

Wannan dabarar a cewar masana za ta taimaka wajen kara wa Guza nisan-kwana ko tsawon-rai.