Rashin haihuwa na sa ana tsangwamar mata a Nijar

Hakkin mallakar hoto none

A Jamhuriyar Nijar, matsalar rashin haihuwa na daga cikin matsalolin da ke haddasa mutuwar aure.

Lamarin dai ya sa matan aure da dama na fuskantar kalubale daga wajen surakai inda suke ganin cewar matan ne suke da matsalar rashin haihuwa.

Wasu matan su kan shafe shekaru ba su samu haihu ba, ko da ya ke daya daga cikinsu ta shaida wa BBC cewa mai gidanta bai damu ba amma mahaifansa sun sa ta a gaba.

Ta kara da cewa shekararta tara ba ta haihu ba, kuma tana ci gaba da yin addu'ar Allah ya ba ta rabo mai albarka.