Zaman dar-dar tsakanin sojoji da jama'a a Zariya

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya wani sabon rikici na neman barkewa tsakanin sojoji da kuma mazauna wata unguwa a Zaria.

Rahotanni sun ce mutane takwas ne aka cafke yayin da sojoji suka shiga yankin Boma na Basawa a Zaria suna harbe-harbe.

Mutanen yankin dai na cewa ba tare da wata takala ba sojoji suka shiga yankin, inda suka yi awon gaba da wasu.

Mutanen na zargin cewa sojoji sun yi musu barazanar aikata makamancin abin da suka aiwatar a Gyallesu, unguwar da Sheikh Al-zakzaky ke zaune.

Sojojin kasar sun musanta muzgunawa mazauna wannan yanki, amma sun ce sun kama wasu a bisa zargin sayarwa da kuma gine-gine a filaye mallakar sojoji.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga rahoton Nura Muhammad Ringim daga Kaduna