Korea ta arewa ta fusata makwabta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Korea ta arewa Kim Jong Un

Kasar Korea ta arewa ta ce ta yi nasarar jarraba wani makaminta na nukiliya, lamarin da ya janyo mata caccaka da suka daga kasashen duniya.

Shugaban Korea ta kudu, Park Geun-Hye ya bayyana gwajin da cewar zunzurutun tsokana ne, kuma gwajin ya saba wa dokokin majalisar dinkin duniya

Shi ma Firayim Minsitan Japan Shinzo Abe ya bayyana gwajin da cewa babbar barazana ce ga kasarsa, kuma kasarsa kyale ba, yayin da China ke cewa ba ta son duk wani abin da zai ta da hankalin al'umar yankin.

Sai dai sanarwar, wadda wani gidan Talabijin din kasar Korea ta arewa ya yi, ta zo ne wasu 'yan sa'o'i bayan wata girgizar kasa mai karfin 5.1 a ma'auni, a kusa da wani sanannen wurin da aka gwada harba makamin nukiliya da ke arewa maso gabashin kasar.

Kasar Korea ta arewar dai ta jarraba makaminta na nukuliya har sau uku a wannan wurin a cikin shekaru 10 da suka wuce, lamarin da ya ja mata suka daga kasashen duniya.

Kwararru a Amurka dai sun ce suna gudanar da bincike a kan wannan ikirari.

Idan an jima ne Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi zama a kan lamarin.