Yunkurin hana amfani da bindiga a Amurka

Hakkin mallakar hoto
Image caption Obama ya yi amanna da cewa matakan za su taimaka wajen kare rayukan jama`a.

Fadar White House ta yi cikakken bayani a kan shirin Shugaba Barack Obama na yaki da bazuwar bindigogi a Amurka.

Za a yi wa dukkan masu sayar da bindigogi rajista a matsayin diloli, kuma wajibi ne su dinga yin bincike a kan masu saya.

Jami'an gwamnati sun ce za a yi gyaran fuska ga dokar kare sirrin jama'a da nufin cire sashen da ya hana bincike a kan bayanan da suka shafi lafiyar masaya bindiga, wato ko sun taba samun tabin-hankali ko a'a.

Shugaba Obama ya yi amanna da cewa wadannan matakai za su taimaka wajen kare rayukan jama'a.

Ya ce shirin ba zai hana bidigogi shiga hannun miyagu baki daya ba, amma zai taimaka wajen kare rayukan jama'a a wannan kasa, tare da yaye wa iyalai tasku ko bakin-ciki sakamakon bazuwar bindigogi a hannun mutanen da ba su dace ba.

Sai dai masu sukar shirin na cewa yana nema ya wuce-gona-da-iri.