Wane ne Sheikh Nimr al-Nimr ?

Hakkin mallakar hoto EPA

Sheikh Nimr al-Nimr, wanda Saudiya ta kashe, a baya fitaccen malamin addini ne daga tsirarun 'yan kasar mabiya Shi'a.

An kama shi ne a shekarar 2012, bayan rikici ya barke a lardin kudancin kasar bayan boren da aka yi na kasashen Larabawa.

A lokacin da aka kama shi, bayan an bi shi a mota a yankin Qatif da ke lardin, an harbe sau hudu a kafarsa - mutane uku ne suka rasa rayukansu a kwanaki ukun da aka shafe ana zanga-zanga bayan an kama shi.

Nimr al-Nimr, wanda a lokacin ya ke da shekaru 50, ya yi fice wajen goyon bayan gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati, a inda mafi yawan 'yan Shi'a su ke korafin ana nuna musu wariya.

Ya samu goyon bayan musamman daga wajen matasa 'yan Shi'a na kasar Saudiyya da kuma Bahrain.

Ya yi munmunar suka a kan akidar Sunni a kasashen biyu.

Bahrain ta murkushe zanga-zanga da mafi yawan mabiya Shi'a a shekarar 2011 da taimakon dakarun sojin ta.

A shekaru 10 da suka wuce, an kama sheikh Nimr a lokuta da dama.

Ya yi zargin cewar 'yan sanda sun yi masa duka a lokacin da ya ke hannunsu.

An tabbatar da hunkuncin kisa a kansa ne a watan Oktobar 2014.

Hakkin mallakar hoto EPA

'Gicciye Shi'

Sheikh Nimr bai taba musanta laifukan siyasa da aka kama shi da su ba, amma kuma magoya bayansa sun ce ya nemi kawai a yi zanga-zangar lumana da hana rikici a kan gwamanti.

A shekarar 2011 , ya shaidawa BBC cewar yana goyon bayan musayar kalamai da hukumomi a kan makamai, kalaman sun fi harsasai tasiri, saboda hukumomi za su ci moriyar amfani da makamai.

A lokacin da aka yi shari'ar sheikh Nimr, wanda ya kai matsayin Ayatollah, a shekarar 2013, masu shigar da kara sun nemi a kashe shi ta hanyar gicciye shi, a Saudiyya hakan ya kunshi fillewa mutun kai sannan kuma a nuna fillalen kan a bainar jama'a.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana cewar ba za a yi masa adalci ba a lokacin shari'ar.

Sun kuma ce ba a ba shi damar samun kulawa da raunukan da ya samu a lokacin da ake kokarin kama shi a watan Yulin shekarar 2012, abin da hukumomi suka musanta.

A cewar jaridar Guardian, a lokacin da ya ke hannun 'yan sanda a shekarar 2012, matarsa Muna Jabir al-Shariyavi, ta mutu awani asibiti a birnin New York, wandan hakan yasa mutane da dama suka tausaya masa kuma suka goyi bayansa.