Hukumar EFCC ta gargadi 'yan canji

Hakkin mallakar hoto efcc

A Najeriya hukumar yaki da cin hanci da rashawa a asar, EFCC ta ce za ta hukunta duk wani dan canji da aka samu da hannu a badakalar dala biliyan biyu da miliyan daya na sayan makamai a kasar.

Hukumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa kafofin yada labarai.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban hukumar EFCC ya shaidawa 'yan canjin da suka kai ma sa ziyara ofishinsa cewa rahotannin da jami'ansa ke ba shi dangane da irin abubuwan da suke cin karo da su a yayinda suke bincike dangane da badakalar sayen makaman ba abune mai dadin ji ba.

Shugaban hukumar EFCC ya kuma nuna takaicinsa a cikin sanarwar game da yadda 'yan canjin ke fitar da makuden kudade zuwa kasasahen waje ba ta hanyar da ta dace ba.

Shugaban 'yan canjin Alhaji Aminu Gwadabe ya shaidawa BBC cewa ba su ji dadin irin abubuwa da aka gano 'yan canjin sun aikata ba.