EFCC ta gargadi masu canjin kudi

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Ibrahim Magu ya ce ba za su bari masu canjin kudaden kasashen waje su rika karya dokokin Najeriya ba.

Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annata, EFCC, Ibrahim Magu, ya ce za a kama duk mai canjin kudaden kasashen wajen da aka samu da hannun wajen yin sama-da-fadi da dala biliya biyu na kudin sayen makamai domin yaki da Boko Haram.

Magu, wanda ya bayyana haka lokacin da kungiyar masu canjin kudaden waje suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja, ya sha alwashin hada gwiwa da 'yan kungiyar domin gudanar da kasuwancinsu yadda ya kamata.

A cewarsa, "Ma'aikata na shun sha gaya min cewa ana hada baki da wasu daga cikinku wajen fitar da kudaden haramun kasashen waje, ganin cewa ba za a bar su su rika cire fiye da dala 300 a injin cire kudi na ATM ba."

"Wasu daga cikinku na da hannu a batun sayen makamai, inda muka samu rahotannin da ke cewa wasunku sun fitar da naira miliyan 500 sau biyu ko sau uku ko ma sau hudu," in ji Magu.

Ya kara da cewa "Na damu sosai da na ga hakan, don haka ya kamata a samu hanyar da za ta nuna yadda kuke gudanar da ayyukanku ta yadda za a magance duk wata cuwa-cuwa".

Tun da fari sai da shugaban kungiyar masu canjin kudaden waje, Alhaji Aminu Gwadabe, ya shaida wa shugaban na EFCC cewa za su ba shi hadin kai domin ganin an tsarkake yadda ake hada-hadar kudi a Najeriya.