Amurka ta bai wa Nigeria motoci masu sulke

Hakkin mallakar hoto US Embassy
Image caption An mika motocin ga sojojin Najeriya a Lagos

Gwamnatin Amurka ta bai wa Najeriya gudunmuwar motoci masu sulke 24 wadanda nakiyoyin da aka binne a hanya ba za su iya lalata su ba, kuma masu kariya daga kwanton bauna.

A cewar sanarwar da ta fito daga karamin ofishin jakadancin Amurka da ke Lagos, wannan mataki ne da zai taimaka wa dakarun sojin Najeriya a yakin da suke yi da 'yan kungiyar Boko Haram.

Sanarwar ta ce darajar motocin sun kai dala miliyan 11, kuma Amurka za ta ci gaba da aiki tare da Najeriya domin kawo karshen kalubalen masu tayar da kayar baya.

"Wadannan motocin alama ce ta Amurka wajen taimaka wa Najeriya da makwabtanta a yaki da kungiyar Boko Haram," in ji sanarwar.

Rikicin Boko haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 18,000 a yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.

A wani mataki na murkushe 'yan kungiyar, gwamnatin Najeriya ta ce za ta soma daukar matasan nan masu taimaka wa sojan kasar wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ka fi sani da civilian JTF, aikin soja.

Hakkin mallakar hoto US Embassy