Kasuwar hannun jarin China ta samu tsaiko

Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Kasuwar hannayen jarin China ta fadi da kashi 7 cikin 100.

An tsayar da hada-hada ta kwana daya a kasuwar hannun jarin kasar China a karo na biyu a cikin wannan makon, sakamakon mummunar faduwar farashin hannayen jarin da fiye da kashi 7 cikin dari.

An rufe kasuwar hannun jarin ne bayan hada-hadar da aka yi ta rabin sa'a a ranar Alhamis din nan.

An kuma rufe kasuwar ne duk da cewa hukumomi a kasar sun zuba biliyoyin dala a kasuwar ranar Litinin.

Dakatar da hada-hadar hannayen jarin a farkon wannan makon ya haifar da faduwar farashin hannayen jari a wasu kasuwanni a duniya.