EFCC ta kama Lawan Ja'afaru Isa

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Shugaban EFCC Ibrahim Magu ya ce za su ci gaba da kama masu hannu a karbar hanci da rashawa.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta kama wani makusancin Shugaba Muhammadu Buhari, wato Birgediya Janar Lawan Ja'afaru Isa, kan zarginsa da hannu wajen karkatar da kudin sayen makamai.

Kakakin EFCC, Wilson Uwajeren, ya tabbatar wa BBC cewa Birgediya Janar Isa yana ofishinsu da ke Abuja, inda ake yi masa tambayoyi.

Sai dai ya ki yin karin bayani a kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Amma wasu rahotanni sun ce ana zargin Birgediya Janar Lawan Ja'afaru Isa da karbar wani kaso cikin dala biliyan biyu da miliyan dari daya da ake zargin Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasa shawara a kan sha'anin tsaro, da yin sama-da-fadi da su.

Kudin dai an ware su ne domin sayen makamai don yaki da kungiyar Boko Haram.

Birgediya Janar Lawan Ja'afaru Isa, tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, shi ne babban jami'in jam'iyyar APC mai mulkin kasar na farko da ya fada hannun hukumar EFCC bisa zargin alaka da badakalar ta sama-da-fadi da kudin makamai.

Wasu na kallon kamun nasa a matsayin babban abin kunya, ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya dade yana hulda da shi.