Shugabannin kasashen da suka yi kuka a bainar jama'a

Ba sabon abu ba ne ga Shugaba Barack Obama na Amurka ya zubar da hawaye a bainar jama'a. A lokacin da yake bayar da sanarwar sabon shirinsa na takaita mallakar bindigogi a kasar, Mista Obama ya tuno harin da aka kai a makarantar firamare ta Sandy Hook a shekarar 2012, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar yara 'yan makaranta 20 da manya shida.

Sai dai ba wannan ne karon farko da ya yi kuka a bainar jama'a ba .

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kuma ba Mista Obama ne dan siyasar da ya taba yin kuka a bainar jama'a ba. Ga 'yan siyasa shida da suka taba zubar da hawaye a bainar jama'a:

Wanda ya zub da hawaye a lokacin gasar Olympic

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya yi kaurin-suna wajen bayyana damuwarsa a fili.

Ya yi kukan-dadi babu kakkautawa a shekarar 2009 bayan an bayar da sanarwar cewa kasarsa ce za ta karbi bakuncin Gasar Olympics ta shekarar 2016.

Sai dai hawayen da ya zubar bai sa kimarsa ta zube a wajen jama'a ba, saboda a lokacin mulkinsa ya kasance shugaban kasar da ya fi ko wane shugaba farin jini a tarihin kasarsa.

Tsoron da Karzai yake ji

Hakkin mallakar hoto Getty

Tsohon shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya ja hankalin kafafen watsa labarai na duniya a lokacin da ya zubar da kwalla a wani jawabi da ya yi a wata babbar makaranta a birnin Kabul a shekarar 2010 saboda halin tabarbarewar tsaro da kasar ke ciki.

Ya yi ta yin kuka a lokacin da yake jawabi a kan rikice-rikicen da kasar ke fama da su, yana mai cewa yana fargaba hakan ka iya tursasawa dansa ya fice daga kasar zuwa kasashen waje.

Kuka a wurin taro manema labarai

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bidiyon wani dan siyasa da ke kuka a lokacinda manema labarai ke masa tambayoyi a kan yadda ya yi amfani da kudade ya yadu kamar wutar-daji a shekarar 2014.

Ryutaro Nonomura ya fashe da kuka a lokacinda aka nemi ya yi cikakken bayani bayani a kan zargin cewar ayi amfani da kudaden jama'a wajen yin tafiye-tafiye.

Sai dai ya dage a kan cewar tafiye-tafiyen aiki ne. Daga sai ya yi murabus a kan batun.

Kukan Sanyi

Hakkin mallakar hoto AP

Idanun shugaba Vladimir Putin ya ciciko da kwalla a lokacinda ya ke yiwa magoya bayansa jawabi a filin Manezhnaya Square da ke birnin Moscow, bayan ya ji sanarwar cewar ya lashe zaben shugaban kasa a kasarsa.

Ganin hawaye a idanun Vladimir Putin, wani yanayi ne sabanin kalon mutun mai taurin rai da ake yi masa, amma kuma mai magana da yawunsa ya ce yanayin sanyin ne ya taba shi, amma ba wai ya yi kuka ba ne saboda ya ci zabe.

Bayyana

Hakkin mallakar hoto Getty

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa a Amurka na shekarar 2008, kwalla ta cikawa Hillary clinton ido a wurin kamfe a New Hampshire, a lokacinda wani ya tambaye ta " me ya sa kike neman shugaban kasa"

Sai muryarta ta fara rawa kuma kwalla ya cika mata ido a lokacinda ta ke amsa tambayar.

Daga baya sai ya yi bayani: " ta ce zan damu idan da banji a jikina cewar wannan muhimmin abu ne kuma ya na da amfani."

Tsohuwar sakatariyar harkokin Amurka ta tsaya takara a shekarar 2008 amma kuma sai shugaba Barack Obama a lokacin zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabanci Amurka a karkashin jam'iyyar Democrats.

Barin ofis

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar 28 ga watan Nuwamba a shekarar 1990, firai ministan wancan lokacin, Margaret Thatcher tayi kwalla a lokacin da ta ke jawabin ban kwana a kofar fadan firai ministan Biritaniya.

Firai ministan Biritaniya mace ta farko, wacca aka yi wa lakabi da mace mai kamar maza, ta ajiye mukamin ta bayan 'yan majlisar zartarwarta sun ki mara mata baya a zaben shugabanci.