'Yan sanda sun kashe dan bindiga a Paris

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an tsaro sun killace wurin

'Yan sandan Faransa sun harbe wani mutum dauke da wuka har lahira a lokacin da yake kokarin shiga wani caji ofis a Paris.

Mutanen da suka shaida lamarin sun sun ce an yi harbi sau biyu ko uku a unguwar Goutte d 'Ore dake arewacin birnin.

Mutumin ya yi kabbara da karfi dauke da bama-bamai a jikinsa.

Hakan dai na zuwa ne shekara daya cif bayan kishe mutane 12 da wasu 'yan bindiga masu tsaurin kishin Islama su ka yi a wani hari da suka kai gidan mujallar nan ta Faransa mai barkwanci, Charlie Hebdo.

Tun da farko, shugaba Francois Hollande ya yi wa jami'an tsaro jawabi luma ya yi gargadin ci gaba da samun barazanar ta'addanci.