An kashe 'yan kabilar Oromo 140 a Ethiopia

Image caption 'Yan Oromo na zargin ana gallaza musu a Ethiopia

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta ce jami'an tsaron kasar Ethiopia sun hallaka 'yan kabilar Oromo fiye da 140, tun lokacin da suka soma zanga-zanga a watan Nuwamba.

Masu zanga-zangar na zargin cewa fadada gine-ginen gwamnati a yankin zai raba manoma 'yan kabilar Oromo da gonakinsu.

Human Rights Watch ta kuma yi kira a saki dan siyasa na kabilar Oromo da aka tsare a watan da ya wuce.

Gwamnatin kasar na zargin 'yan Oromo din da alaka da kungiyoyin ta'adda.

A watan da ya wuce, jami'ai sun ce an kashe mutane biyar tare da wasu jami'an tsaro a lokacin zanga-zangar.