Tallafawa matan 'yan sandan da Boko Haram ta kashe

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar matan 'yan sandan a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rabawa 'ya'yanta da aka kashe mazajen su sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram kayan abinci domin tallafawa rayuwarsu.

Kungiyar ta ce ta yi hakan ne domin fitar da matan daga mummunan halin da suke ciki.

Haka kuma kungiyar ta ce za ta yi tsaiwar-daka domin ganin hakkokin 'yan sandan da suka mutu ya fito.

Sai dai wasu matan 'yan sandan da mazajensu suka mutu a hare-haren Boko Haram din sun koka da mawuyacin halin da suka shiga sakamakon rashin biyansu hakkokin mazajensu.

Sun ce saboda rashin biyan su hakkokin mazajensu, ba sa iya ci gaba da dawainiyar gidajensu, kamar biyan kudin makarantar yara da sayen kayan abinci.

Don haka ne ma suka bukaci hukumomin 'yan sanda da su yi kokarin biyansu hakkokin mazajensu domin yaye musu wahalar da suke sha.