'Yan adawar Nijar da aka tsare sun koka

A jamhuriyar Nijar, jam'iyar MNSD Nasara da wasu lauyoyin kasar sun nuna damuwa matuka, dangane da halin da wasu 'yan siyasa, galibi na bangaren adawa ke ciki, bayan da hukumomin kasar suka kama su, sama da kwanaki 20 da suka gabata.

Tun da aka kama 'yan siyasar dai, ko lauyoyinsu ba su samu ganawa da su ba, lamarin da lauyoyin suka ce ya keta hakkin dan adam.

Lamarin ya biyo bayan binciken da gwamnatin ta ce ta kaddamar ne domin gano mutanen da ke da hannu a yunkurin juyin mulkin da ta bankado a cikin watan Disambar da ya gabata.

Kawo yanzu hukumomin Nijar din ba su yi wani karin bayani ba dangane da kamen 'yan siyasar da kuma rashin bayar da damar ganin nasu.