'Rikicin shugabanci a jam'iyyar PDP'

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption 'Yanzu haka dai jam'iyyar ba ta da shugaba da mataimakin Shugaba'

A Nigeria, bisa ga dukkan alamu, har yanzu ba a kai ga warware rikicin shugabanci da ya dabaiye jam'iyyar adawa ta PDP ba.

A kwanakin baya ne dai wata kotu a Abuja ta zartar da hukuncin cewa shugaban riko na Jam'iyyar, Uche Secondus ba shi da hurumin ci gaba da zama a kan mukaminsa, lamarin da ya kara dagula al'amuran shugabancin jam'iyyar.

Barrister Ahmed Gulak, tsohon mai bai wa shugaban Nigeria Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa wanda kuma shi ne ya shigar da karar kalubalantar Uche Secondus, ya fadawa BBC cewa yanzu jam'iyyar ba ta da Shugaba da kuma mataimakin Shugaba.

Ya kara da cewa, "Kotu ta bai wa PDP kwanaki goma sha hudu da ta zabe ni ko duk wani mambanta daga yankin arewa maso gabashin kasar na a matsayin shugaba, amma wa'adin ya wuce ba ta yi ba. Don haka yanzu jam'iyya ba ta da shugaba".

Tuni dai hukumar EFCC a Nigeria ta tsare kakakin jam'iyyar PDPn Oliseh Metuh bisa zargin yana da hannu a badakalar kudaden sayen makamai.