Shadda mai wanke kanta sau daya a shekara

Image caption Shadda mai wanke wa mutane kashi da kanta

A ci gaba da baje kolin kayan latironik a birnin Las Vegas na Amurka, an gabatar da wani mazaunin shadda na zamani wanda yake bude kansa da zarar mutun ya tunkaro, kuma yake kore bayan-gidan da aka yi da kansa.

Kazalika, mazaunin shaddar ya na wanke duwawun mutumin da ya yi bayan-gida, da ruwa mai dumi da kuma wata iska da take busar da ruwan da take shigowa daga mazaunin shaddar.

Duk da cewa farashin mazaunin shaddar ya kai dala dubu tara da dari takwas, an sayar da fiye da miliyan 40 daga gabatar da shi a kasuwa.

Kamfanin Toto mai kera kayan amfani a ban-daki ya ce har yanzu, ba a kammala aikin kirkiran mazaunin shaddar ba.

Mazaunin shaddar ya na amfani da ruwa mai dauke da magungunan kashe cututtuka wajen wanke wa mutane bayan-gidan da suka yi yayin da suke zaune.

Mai magana da yawun kanfanin Toto, Misis Lenora Campos ta ce da zarar mazaunin shaddar ya kore bayan-gidan da aka yi, sai ya koro wani ruwa mai dauke da sinadaren kashe cututtuka da zai wanke mazaunin shaddar.

Bugu da kari kuma, mutane ba su bukatar wanke mazaunin shaddar har na tsawon shekara daya.

Lokacin da BBC ta tambayi wasu masu otal-otal a Las Vegas ko zasu yi amfani da sabon mazaunin shaddar, sai suka yi gum, ba su ce komai ba.

Sai dai wani kwararre daga cibiyar bincike ta Forrester, Frank Gillett ya yi gargadin cewa, sabon mazaunin shaddar, ba yana nufin kwata-kwata mutane ba za su rika tsaftace ban-dakin su ba ne.