Kiir ya nemi gafara daga al'ummar kasar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Kiir ya sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

A karon farko, Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu, ya nemi gafara daga al'ummar kasar, a kan abin da ya kira wahalar ba gaira ba dalilin da suka jure tsawon shekaru biyu saboda tashin hankali.

"Ina so, tsakani da Allah in nemi gafarar a wurin mutanen Sudan ta Kudu, saboda bakar wahalar da ku da kasarmu kuka tsunduma a cikin shekaru biyun da suka wuce," in ji Kiir.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne ga magoya bayan jam'iyyar SPLM da ke jan ragamar mulkin kasar, inda ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da wannan taro domin kaddamar da wani shirin da zai kasance cike da tarihi wajen yafewa juna domin mantawa da abubuwan da suka wakana.

To amma ya kara da cewar za a hukunta dukkanin wadanda ke da alhakin aikata laifuka.